Papers by Faisal Lema
Thesis Chapters by Faisal Lema

Kundin Digiri Na Daya, 2023
TSAKURE
Wannan bincike ne da aka gabatar kan Salo da Sarrafa Harshe a cikin littafin Wasan Kwaikw... more TSAKURE
Wannan bincike ne da aka gabatar kan Salo da Sarrafa Harshe a cikin littafin Wasan Kwaikwayon Daqiqa Talatin na Ado Ahmad Gidan Dabino MON. Dalilin gudanar da wannan bincike shi ne don cike giɓin da ake da shi na rashin gudanar da bincike a kan wannan littafin “Daƙiƙa Talatin”. Alal haƙiƙa salo da sarrafa harshe babban ɓangare ne da ya kamata a yi nazari, wannan ne ya ƙara mani ƙwarin guiwar gudanar da wannan bincike. Manufar wannan bincike ita ce Don Fito da Salon Sarrafa Harshe daga littafin “Daƙiƙa Talatin” da kuma Fito da irin gudunmuwar da salo ke bayarwa a cikin littattafan wasan kwaikwayo, fito da muhimmancin wannan littafi ga rayuwar al’umma domin nazari. Babban muhimmancin wannan bincike shi ne, don ya taimaka wa masu bincike ta hanyar laƙantar wasu abubuwa da suka shafi rubutun wasan kwaikwayo kamar salo da jigo domin fito da wasu manufofi ko alfanu daga cikinsu. Binciken zai taimaka wajen ƙara faɗaɗa ilimi wanda zai amfanar ta yin nazarin wannan littafin. Daga cikin hanyoyin da aka bi wajen gudanar da wannan bincike sun haxa da: Ziyarar xakunan karatu na cikin makaranta da kuma na waje, da kuma tattaunawa da masana, domin samun qarin haske lya ta yadda za a gudanar da wannan bincike, da karantawa daga rubutattun bayanai da suka haxa da kundayen bincike, da bugaggun littattafai, da muhallu da takardun ilimi da sauran su. Sakamakon wannan bincike shi ne an samu salo da sarrafa harshe a cikin littafin wasan kwaikwayon Daqiqa Talatin, in da aka gano marubucin ya yi amfani da salon labartawa a cikin littafin, hakan ya sanya salon ya zamo miqaqqen salo mai armashi, sabo da babu kon gaba kon baya a cikin littafin.
Uploads