Papers by Yusuf Jibril

Tsakure: Harshe yana ɗaya daga cikin tarin baiwar da Allah (S.W.T) ya hore wa ɗan Adam, wanda ake... more Tsakure: Harshe yana ɗaya daga cikin tarin baiwar da Allah (S.W.T) ya hore wa ɗan Adam, wanda ake amfani da shi wajen sadarwa musamman ta hanyar yin magana ko waƙa ko hira da dai sauransu. Harshe yana daga cikin muhimman abubuwan da ake amfani da su a fagen siyasa, wanda hakan yakan taimaka wurin samun nasara ko akasin haka. Mawaƙan siyasa da dama sukan yi amfani da irin baiwar da Allah ya ba su na iya sarrafa kalmomi a waƙe wajen yabon jam'iyyarsu ko 'ya'yanta, domin ɗaga su da tallata su ga sauran jama'a. Haka kuma da irin wannan baiwar ce suke amfani wajen sukar 'yan adawa da jam'iyyar adawar domin dusashe haskensu. Wannan takarda ta yi nazarin yadda ake amfani da waƙoƙin siyasa wajen yabon jam'iyya da shugabanninta da kuma ƙoƙarin daƙushe hasken jam'iyyar adawa da magoya bayanta. A ƙarshe binciken ya gano cewa harshe wani ginshiƙi ne wajen tafiyar da al'amuran siyasa domin da shi ne ake tallata jam'iyya ko ɗan takara har su karɓu ga jama'a, kuma da shi ne ake kushe su ta hanyar suka wanda hakan kan rage musu farin jini ko ya janyo su rasa magoya baya. A cikin nazarin an riƙa kawo misalai daga baitocin waƙoƙin siyasa domin kafa hujja.

Rayuwar matasa a wannan zamani ya zama abin takaici, kasancewar an yi sakaci baqin al'adu sun yi ... more Rayuwar matasa a wannan zamani ya zama abin takaici, kasancewar an yi sakaci baqin al'adu sun yi wa al'adun Hausawa kutse, yadda har ta kai ga al'adunmu da muka gada tun kaka da kakanni sun fara yi mana nisa, kuma har ta kai ga sauye-sauyen sun fara barazana ga zaman lafiyarmu. Manufar wannan takarda ita ce gano sauye-sauyen xabi'u tsakanin matasa, da kuma irin barazanar da yake yi ga zaman lafiya. Takardar ta yi qoqarin kawo bayanai kan matasa a jiya wato a rayuwar gargajiya, sannan kuma an kawo bayanai kan rayuwar matasa a yau da yadda zamani ya yi tasiri a kansu. Daga bisani an zayyano irin miyagun halayen da matasa kan tsunduma ciki da kuma abin da yake haifarwa musamman yadda xabi'un matasan kan riqa yin barazana ga zaman lafiya da kwanciyar hankalin al'umma. Sannan kuma an yi qoqarin gano dalilan da suke haifar da waxannan sauye-sauyen xabi'un. A qarshe takardar ta yi qoqarin bayar da shawarwari kan hanyoyin da ya kamata a bi domin magance waxannan matsaloli domin samun kai wa ga tudun mun tsira.
Matasa Da Miyagun Dabi'u: Barazana Ga Zaman Lafiyar Kasa.
Conference Presentations by Yusuf Jibril

Tsakure
Kowace jam’iyyar siyasa da aka kafa tun daga samun ‘yancin kai zuwa yau an kafa ta ne bis... more Tsakure
Kowace jam’iyyar siyasa da aka kafa tun daga samun ‘yancin kai zuwa yau an kafa ta ne bisa wasu ayyanannun manufofi da tsare-tsare waxanda jam’iyyar za ta bi, waxanda kuma da su ne za ta riqa tallata hajarta ga al’umma domin su amince su zave ta. Yawanci waxannan manufofin su ne kan zamo alqawuran da ‘yan siyasa ke yi wa al’umma don neman quri’unsu. Ire-iren waxannan alqawura ba su wuce hanyoyin jin daxi da kyautata rayuwar al’ummar ba. Kowace jam’iyya takan tsara manufofinta a rubuce, daga bisani sai a raba wa jama’a, wasu kuma sai dai idan an tafi yaqin neman zave za su ji manufofin jam’iyyar a bakin ‘yan takara ko ‘yan siyasa ko magoya bayansu ko kuma mawaqansu da na jam’iyya. Manufar wannan takarda ita ce zaqulo manufofin jam’iyyar PDP daga bakin marubuta waqoqin Hausa, domin ganin irin rawar da marubuta waqoqin suke takawa wajen tallata jam’iyyun siyasa ga al’umma a wannan qarni da muke ciki, wato qarni na 21.
Haka kuma, kasancewar yawancin manufofi da tsare-tsaren jam’iyyun siyasa akan raba su ne a rubuce cikin kundin manufofin jam’iyya (manifesto), wannan nazari zai yi qoqari fito da irin rawar da rubutattun waqoqoin siyasa suke takawa a fagen siyasa wajen tallata manufofin jam’iyya a wannan qarni da muke ciki, wato qarni na 21.
Uploads